
Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC) ta tsare tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, kan zargin badakalar cire kuɗaɗe da darajarsu ta kai naira biliyan 189.
Majiyoyi daga cikin EFCC sun tabbatar da cewa an tsare Tambuwal ne bisa zargin fitar da kuɗi a bainar jama’a, abin da ya sabawa dokar hana safarar kuɗi masu nauyi ta shekarar 2022.
Wani jami’in hukumar da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya isa ofishin EFCC da ke Abuja a ranar Litinin, domin amsa tambayoyi kan lamarin.
Sai dai, kakakin hukumar, Dele Oyewale, bai bayyana cikakken bayani ba kan tsarewar.
Aminu Waziri Tambuwal ya yi wa Jihar Sokoto mulki daga 2015 zuwa 2023, kafin ya zama Sanata a Majalisar Dattawan Ƙasa