
Hukumar EFCC ta cafke Murja Kunya bisa zargin wulakanta takardar Naira.
Rahotanni sun ce shahararriyar ‘yar Tik tok ta shiga hannun jami’an hukumar ne a ranar Asabar a Kano.
Aminiya ta rawato cewa, Jami’an na EFCC sun kama Murja kimanin makonni uku da suka gabata, amma ta tsere daga beli kafin sake kama ta a ranar Asabar din.
Majiyar hukumar ta ce, idan bincike ya kammala, za a gurfanar da ita a kotu domin fuskantar hukunci bisa laifin da ake zarginta da aikatawa na wulakanta takaradar kudin.
A kwanaki baya shugaban hukumar reshen jihar ya yi gargadin soma kamen masu wulankanta tarkaradar kudin tare da hukunta su.
Murja Kunya ta yi kaurin suna tun bayan fara amfani da kafafen sada zumunta a matsayin abin barkwanci, kafin daga bisani ta mayar da shi dandalin sana’a
A tsawon lokaci, ta shahara musamman a TikTok, inda take amfani da sunan “Yagayagamen,” duk da cewa a bayan nan ta jawo ce-ce-ku-ce a kanta tare da shiga hannun hukumar Hisbah a Kano a bisa zargin yada badala.
A bayan nan dai hukumar ta EFCC ta cafke wasu abokan sana’ar Murja ’yan TikTok irinsu Alamin G-Fresh da Ashir Idris kan makamancin wannan zargi na wulaƙanta takardun kuɗi.