
Hukumar EFCC ta kama tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar Kazaure da Gwiwa da ‘Yan Kwashi, Honorabul Gudaji Kazaure bisa zarginsa da karbar Naira miliyan 70 daga Godwin Emiefele.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, Hukumar EFCC ta kama Gudaji ne a ranar a Laraba jim kadan bayan da wata babbar kotu a Kano ta janye kariyar kamashin da aka bayar.
Rahotannin farko sun ce, EFCC ta kama Gudaji Kazaure ne bayan da ya masa gayyatar da ta yi masa a ofishinta na jihar Kano don amsa wasu tambayoyi dangane da zargin da ake yi masa na shigar wasu miliyan 14 asusunsa na banki a shekarar 2019.
Tsohon dan majalisar yayi kaurin suna a wajen caccakar masu cin hanci da rashawa, ta kuma ce ya fara karbar naira miliyan 20 ta hannun Mista Erik, wani na hannun daman Emefiele domin sayen ragon layya.
Majiiyar ta kuma ce, Gudaji ya sake karbar miliyan hamsin a matsayin gudunmawa daga Emefeile sakamakon gobarar da Gudajin yayi a gidansa a Abuja.
A halin yanzu Gudaji yana tsare a ofishin EFCC dake Kano kuma ana iya garzayawa da shi Abuja domin fuskantar tuhuma.
A watan disambar 2022 Kazaure ya zargi Emefele da almundahana inda ya zarge shi da wawure sama da Naira Triliyan 89.1
Sannan ya kuma yi zargin cewa, da gangan aka hana shi gabatar da rahoton share fage da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin nazarin kudaden harajin da CBN yake karbar na Stamp duty.
A wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ta fitar a wacce Kakakinta Garba Shehu ya sa hannu a lokacin, ya musanta zargin tare da cewa, tuni aka rushe kwamitin .