
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa EFCC ta kama ƴan damfara 792 a birnin Lagos
Wadanda aka kama sun haɗa da Larabawa da ‘ƴan China da kuma ‘yan kasar Philippines.
Daraktan Hulɗa da Jama’a na hukumar Wilson Uwajaren ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a babban ofishin hukumar dake birnin .

Kakakin ya ce, mutanen da aka kama sun shahara wajen damfara ta yanar gizo, inda suke ɓoye kamanninsu tare da gabatar da soyayya ta ƙarya domin yaudarar jama’a a sassan duniya.
Hukumar ta cafke ‘ƴan damfarar ne a ranar 10 ga watan Disamba a wani katafaren gida mai hawa bakwai kuma mai lamba 7, a unguwar Jolayemi da ke Victoria Island a birnin Lagos.
Hukumar ta ce, ta shafe tsawon watanni tana tattara bayanai kafin ƙaddamar da samamen.
“Ƙwararrun ‘ƴan damfarar na ɗaukar ‘ƴan Najeriya aiki tare da biyan su albashin sama da Naira dubu 200 a kowanne wata domin taya su gudanar da ayyukansu na damfara a sassan duniya daban-daban.

“An zuba manyan kwamfutoci na alfarma kuma na zamani a cikin wannan katafaren ginin, yayin da aka gano layukan waya sama da 500 a hawa na biyar kaɗai”. Inji shi
Ya kuma ce, Amurkawa da ‘ƴan Canada da Mexico su ne suka fi faɗawa komar waɗannan kwararrun ƴan damfarar.
Kamfanin ƴan damfarar na bai wa ƴan Najeriyar da ya ɗauka aiki layukan ƙasashen Turai musamman daga Jamus da Italiya don gudanar da aikin damfarar cikin sauki.
