Hukumar EFCC ta ayyana neman wasu jami’an kamfanin CBEX waɗanda take zargi da hannu a damfarar ƴan Najeriya miliyoyin kuɗaɗe a wani tsarin zuba kuɗi don neman riba mai tsoka.
Wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta, ya ce tana zargin mutanen takwas da yaudarar jama’a su zuba kuɗi don samun riba – daga bisani suka tsere da kuɗaɗensu.
Hukumar ta bayyana sunayen mutanen da Seyi Oloyede da Emmanuel Uko da Adefowora Oluwanisola da kuma Adefowora Abiodun Olaonipekun.
Sauran waɗanda take nema ‘ƴan ƙasashen waje sun haɗa da Johnson Otieno da Israel Mbaluka da Joseph Kabera da kuma Serah Michiro.
Hakan na zuwa ne bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bai wa jami’an EFCC ɗin damar kame da kuma tsare mutanen da aka samu da hannu wajen yaɗa tsarin na CBEX.
