
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa zai goyi bayan waɗanda ke goyon bayan Shugaba Bola Tinubu, ya kuma buƙaci mazauna yankin da su goya wa waɗanda gwamnati za ta saurare su baya.
Wike ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yaba wa tsohon Sanata mai wakiltar Birnin Tarayya Abuja, Philip Aduda da kuma shugaban Ƙaramar Hukumar Abuja AMAC, Christopher Maikalangu a lokacin ƙaddamar da aikin samar da ruwan sha na Lot 2 a yankin Karu, a ranar Alhamis.
Ministan ya yaba wa mutanen biyu bisa irin ƙoƙarin da suke yi na samar da ci gaba ga jama’a, yayin da ya yi alƙawarin gina titin kilomita 2 a yankin Karu, bisa buƙatar Aduda ya kuma ƙara da cewa zai goyi bayan waɗanda suka ci gaba da marawa gwamnatin Tinubu baya.
Daga nan kuma ya yaba wa shugaban AMAC, Maikalangu a matsayinsa na gwarzo kuma mai ƙoƙari, inda ya bayyana cewa ya yi amfani da damarsa na gwamnati wajen kai wasu ayyuka ga mazauna yankin Ƙaramar hukumar, inda ya ƙara da cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya buƙata (Maikalangu) don ya sake lashe zaɓen kujerar shugaban ƙaramar hukumar.