Gwamnatin jihar Ondo ta sanar da cewa daga yanzu za ta fara yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane.
Babban attoni janar na jihar, Kayode Ajulo shi ya bayyana haka a birnin Akure ranar Asabar bayan taron majalisar zartaswa na jihar.
Ya bayyana cewa za a rushe duka gine-gine da kuma wurare da masu garkuwa ke amfani da su wajen aikata laifuka bayan samun umarnin kotu, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Ajulo ya ƙara da cewa za a yi wa dokar yaƙi da ayyukan masu garkuwa a jihar garambawul, domin saka batun hukuncin kisa ta hanyar rataya a cikin ta.
Ya ce sun kuma damu kan ƙaruwar ayyukan ƙungiyoyin asiri a jihar, inda ya ce za su yi duk abin da ya kamata wajen magance batun.
Ondo ta bi sahun jihar Edo wadda ta bijiro da irin wannan hukunci ga masu garkuwa a watan Afrilu, da nufin magance matsalar garkuwa da ta yi kamari.
