
Gwamnatin Sojin Sudan karkashin Abdul Fateh Al Burhan ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawa UAE da hannu a yakinta da Kungiyar RSF, ta kuma sha alwashin kai ta Kotun Aikata Manyan Laifukana yaki ICC
Yaƙin basasar ƙasar da ake gwabzawa tsakanin gwamnatin da dakarun RSF ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane.
Sudan ta ce, akwai sa hannun sojojin Dubai a kisan kiyashin da aka yi wa mutane a garin Masalit.
Cikin zargin gwamnatin Sudan din ya hada da bai wa kungiyar RSF tallafin soji da kuɗi da kuma goyon baya a siyasance.
Ta kuma buƙaci kotun ICC ta hana UAE shiga al’amuran ƙasar.
Sai dai Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta musanta zargin, inda ta buƙaci kotun ta yi watsi da ƙarar, wadda ta bayyana da mara tushe.