Wata ƙungiya mai zaman kanta a Najeriya ta yi Korafin Kan yadda dimukiraɗiya Najeriya ke tafiya.
Kungiyar mai suna ‘Nigeria Unite’, ta bayyana hakan ne a wata wasika da ta rubuta ga ƙungiyar ƙasashen Turai EU.
Kungiyar ta gabatar da ƙorafin ne a kan yadda ake yiwa dimokiraɗiya karan tsaye a ƙasar da kuma yankin Sahel.
“Muddin duniya ta zuba ido ba ta ɗauki mataki a kan abin da ke faruwa ba, babu tabbas dimokiradiyar Najeriya, wadda ita ce mafi girma a Afirka, na iya rugujewa.
“Wanda hakan ka iya haifar da ƙaurar mutanen yankin zuwa Turai a matsayin baƙi. In ji kungiyar.
Wasikar Sunday Daniel ne ya rattabawa hannu, ya kuma rabawa manema labarai a ranar Alhamis.
“Bayan rugujewar dimokiradiya a ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar, yanzu haka ta Najeriya na tangal tangal, saboda irin matakan da gwamnatin ƙasar ke ɗauka na murkushe ƴan adawa”. In ji sanarwar.
Ƙungiyar ta kuma zargi gwamnatin Najeriya da ɗaukar matakan murƙushe ƴan adawa da zummar mayar da ƙasar, ƙasa mai jam’iyya guda, ta hanyar amfani da ministan Abuja.
Kungiyar ta zargi Nyesome Wike da kama- karya tare da goyan bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Sanarwar Ƙungiyar ta kuma bayyana yadda ministan na Abuja ke amfani da muƙamin sa wajen haifar da ruɗani da kuma murkushe manyan jam’iyyun adawar ƙasar irin su PDP da LP da kuma ADC da zummar ganin shugaba Tinubu ya samu wa’adi na biyu ba tare da wata hamayya ba.
Ƙungiyar ta kuma kara da cewa muddin Wike ya samu nasara a kan wannan aniyar ta sa, wadda ta ƙunshi barazana ga ƴan adawa da gabatar da cin hanci wajen tilasta musu sauya sheƙa da haifar da ruɗani.
Matakin da ta ce, na iya haifar da tashin hankalin da zai shafi jama’ar ƙasar miliyan 250 da kuma tilastawa wasu ƴan ƙasar ƙaura zuwa Turai da Amurka domin samun mafaka.
Ƙungiyar ta buƙaci ɗaukar matakan gaggawa daga EU da AU da Amurka da kuma Birtaniya domin magance matsalar.
Ta hanyar sanya takunkumi a kan minista Wike wajen hana shi tafiye tafiye ƙasashen duniya.
- Zargin kisan kiristoci: Aikin jam’iyyun hamayya da Ƙasashen Waje ne – Wike
- 2027: Wike ya magantu game da takarar Jonathan da Turaki a PDP
