
Gwamnatin tarayya ta bayyana goyon bayanta ga shirin hukumar WAEC na mayar da jarabawar kammala sakandare daga takarda da biro zuwa tsarin rubutu ta kwamfuta, watau CBT daga shekarar 2026.
Ministan Ilimi Tunji Alausa ne ya bayyana haka a Abuja yayin wani taron wayar da kai da ya haɗa da majalisun dokoki da sauran masu ruwa da tsaki.
Alausa ya ce, sabon tsarin zai ƙarfafa ingancin ilimi a Najeriya tare da dakile matsalar satar amsa.
A cewarsa, duk da adawar da aka samu daga wasu bangarori a farko, gwamnati ta yanke shawarar mara wa tsarin baya domin kawar da tsohuwar dogaro da rubutun takarda da biro.
Shugaban ofishin WAEC na ƙasa Amos Dangut ya ce, an fara gwajin wannan sauyi tun a shekarar 2024 kan ɗaliban da suka rubuta jarabawar kuɗi mai zaman kanta, kuma sakamakon ya nuna nasara fiye da tsarin takarda.
Dangut ya tabbatar da cewa hukumar za ta samar da kayan aiki da kuma hanyoyin koyar da ɗalibai yadda tsarin yake domin kada wani ya yi ƙasa a gwiwa.
Ya ƙara da cewa WAEC ta riga ta nuna ƙarfin gudanar da jarabawa a wuraren da ke da ƙarancin intanet ba tare da matsala ba.
A cewarsa, sakamakon ɗaliban da suka rubuta jarabawar gwajin ta kwamfuta ya fi kyau idan aka kwatanta da wanda aka saba samu a tsarin takarda, lamarin da ya ƙara tabbatar da dacewar sabon tsari.