Rahotanni sun bayyana Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shayarwa suka gudanar da zanga-zangar lumana a Gusau babban birnin jihar Zamfara sakamakon ƙaruwar hare-haren ƴanbidida a jihar.
Matan waɗanda suka fito daga garin Jimrawa na yankin ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda sun koka kan yadda suka ce ƴanbindiga na ci gaba da addabarsu da jerin hare-hare tare da sace musu mutane.
Zanga-zangar matan na zuwa aƙalla mako biyu bayan wasu zanga-zanga biyu da aka gudanar a brnin na Gusau, bayan da masu zanga-zangar suka yi iƙirarin cewa hare-haren ƴanbindigar sun kashe fiye da mutum 100 a ƙauyukan Mada da Ruwan Baure da fegin Baza da Lilo da kuma Bangi.
Mazauna jihar sun ce rashin hanyoyi masu kyau na kawo wa jami’an tsaro tarnaƙi wajen isa yankunan, lamarin da ke bai wa ƴanbindigar damar cin karensu babu babbaka.
