
Zauran Daraktocin Mulki na kananan hukumomi 44 na jihar Kano ya bukaci Daraktocin kananan hukumomin jihar da su yi riko da amana da kuma jajircewa wajen tafiyar da ayyukan ci gaban tattalin arzikin yankunansu.
Shugaban Zauren, kuma Daraktan Mulki na Karamar Hukumar Bagwai Alhaji Aminu Mukhtar ne ya bayyana hakan a lokacin tattaunawarsa da manema labarai akan ci gaban da Ma’aikatar ta samu wajen tafiyar da ayyukan gwamnatin jihar Kano.
Alhaji Aminu Mukhtar ya ce, gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kawo manufofi da shirye-shirye na kyautatawa ma’aikata da inganta ilimi da kula da lafiya da Samar da ingantattun hanyoyin mota domin bunkasa tattalin arzikin al’ummar jihar nan.
Jami’in yada labarai karamar hukumar Bagwai Shehu Bello Shanono ya rawaito cewa, Daraktan Mulkin ya yi kira ga al’ummomin kananan hukumomin Kano su rungumi ayyukan raya kasa na gwamnatin Kano a matsayin kayansu, su kuma kula da su domin amfanin kansu.