

Matatar mai ta Dangote na shirin gina wani rumbun ajiyar man fetur da dizel a Walvis Bay, ƙasar Namibiya, domin sarrafawa da sayar da ganga miliyan 1.6 na mai a ƙasashen kudancin Afirka.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa ana sa ran ma’adanar za ta zama babbar cibiyar hada-hadar man fetur ga ƙasashen Botswana, Namibiya, Zambiya da Zimbabwe.
Kazalika, kamfanin Dangote na nazarin shirin kai man fetur zuwa Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, domin faɗaɗa kasuwancin sa a yankin.
Wani jami’in hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Namibiya ya tabbatar da shirin gina rumbun ajiyar, inda ya ce ana shirin kafawa a yankin Walvis Bay.
A baya-bayan nan, matatar Dangote ta fara fitar da man fetur zuwa nahiyar Asiya, lamarin da ke nuna ƙarfin faɗaɗa kasuwancin matatar daga yammacin Afirka zuwa sassan duniya.