Dangote ya ƙaddamar da shirin tallafawa ɗaliban Najeriya.
Sabon shirin ilimi zai ci naira triliyan guda da miliyan dubu 350 a cikin shekaru 10.
Shirin da aka kaddamar ya nuna cewar, attajirin zai bada gudumawar kashi 25 bisa 100 na dukiyarsa ga Gidauniyar.
An ƙaddamar shirin a ranar Alhamis a Lagos.
“A kowacce shekara zan kashe naira biliyan 100 wajen bada gudumawar da ta shafi bada ilimi wadda za ta shafi miliyoyin matasa daga kowanne saƙo na Najeriya.
“A ƙarƙashin za’a ƙashe sama da naira triliyan guda a cikin shekaru 10, don horar da yara da mata a makarantu daga matakin sakandare zuwa jami’oi kowacce shekara.” In ji shi.
Shirin zai shafi ɗalibai 20,000, yayin da wasu 5,000 kuma za’a dinga koya musu sana’oi.
An kuma sanya wa kowanne shiri sunan ƴaƴan Dangoten, wato Mariya da Halima da kuma Fatima.
Daliban za su fito ne daga kowacce ƙaramar hukuma dake Najeriya ba tare da nuna banbanci ba.
Kimain dalibai 45,000 za su dinga cin gajiyar shirin daga shekarar 2026, abinda zai kai ɗalibai 155,000 nan da shekaru hudu masu zuwa.
