Attajirin ya gana da shugaban ne kan batun zuba jari a kasar da kulla harkokin cinikayya da tsakaninta da Najeriya
Hamshakin attajiri dan Najeriya Aliko Dangote ya gana da Shugaban kasar Guinea a Conakry Janar Mamady Doumbouya,
Attajiri ya gana da shugaban ne a ranar Talata a fadar shugaban kasa a Konakry babban birnin kasar.
TRT ta rawaito cewa, Attajirin ya tattauna da shugaban ne kan yadda za a karfafa cinikayya tsakanin Guinea da Nijeriya.
Rahoton ya ce, tattaunawar ta mayar da hankali ne kan kulla yarjejeniyar kasuwanci a fannonin man fetur da noma da kuma aikin banki.
Aliko Dangote dan asalin jihar Kano shine an ayyana shi da cewa shi ne ma fi arziki a nahiyar Afrika.