Dan majalisar dokokin Kano mai wakiltar karamar hukumar Gabasawa a Zakariyya Abdullahi Nuhu, ya bukaci gwamnatin jihar da ta samar da kwalejin koyan aikin gona a Gabasawa.
Hakan na kunshe ne cikin wani kuduri da Dan majalisar ya gabatar a zaman zauren na yau.
A cewar zakariya idan aka samar da kwalejin a yankin za ta tainaka wajen bunkasa ilimin aikin noma da tattalin arziki a gaba daya mazabu 11 dake karamar hukumar kasancewar fiye da kaso 60 na mutanen yankin manoma ne.
Zakariyya yace gwamnati zata iya amfani da wata makarantar kwana ta ‘yan mata a yankin domin samar da kwalejin, wadda a baya dalilan tsaro yasa aka rufe ta, sai dai duk da bude ta da akayi yanzu daliban cikin ta basu wuce guda 30 ba.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewar, majalisar ta ce zata aike da bukatar mambar nata ya zuwa bangaren zartarwa domin daukar matakin daya dace.
