
Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Ɗambatta da Makoda, Hamisu Ibrahim Chidari, ya ƙaddamar da aikin gina sabon titi daga ofishin ‘ƴan sanda na Ɗambatta zuwa garin Gwarabjawa.
Da yake ƙaddamar da aikin hanyar Hamisu Ibrahim Chidari, ya bayyana cewa wannan aiki yana cikin kudurinsa na ci gaba da inganta rayuwar al’umma, tare da samar da muhimman ayyukan more rayuwa ga yankin.
A nasa jawabin dan kwangilar da zai gudunar da aikin hanyar, Injiniya Auwal Shu’aibu, ya tabbatar da cewa kamfaninsu zai gudanar da aiki mai inganci tare da kammalawa cikin lokacin da aka tsara, domin ganin al’ummar yankin sun amfana.
Wakilinmu Ishaq Sani Dambazau ya rawaito cewa dan majalisar na cewa wannan aiki na daga cikin kudirinsa na samar da ayyukan ci gaban yankin ta hanyar ayyukan raya ƙasa