
Hukumar Kula da Hada-hadar Hannayen Jari ta Kasa (SEC) za ta bincike kamfanoni 79 da ake zargin suna gudanar da ayyukan damfara ta hanyar yi wa mutane alkawarin ribar da ta fi karfin gaskiya kan jari da suka zuba ake kira ‘Ponzi scheme’
A sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce binciken ya shafi kamfanoni da dama da ke aiki a sassa daban-daban na Najeriya ciki har da wani kamfani mai suna FF Tiffany, wanda ake zargi da zambatar dubban masu zuba jari a kasar.
Hukumar ta kuma ce, wannan kamfani yana daga cikin wadanda ke gab da fuskantar matakin doka, yayin da ake ci gaba da tattara hujjoji kan yadda ya yaudari mutane da batutuwan da suka shafi harkokin kudin su.
SEC ta kara da cewa ta fara gangamin wayar da kai a cikin al’ummomi daban-daban don fadakar da jama’a game da hadurran irin wadannan salo na damfara.
Hukumar ta bayyana wadannan ayyuka na Ponzi a matsayin barazana ga amincewa da fannin hada-hadar kudi a Najeriya, inda ta ce hakan na iya janyo koma baya ga sha’awar saka jari a cikin tattalin arzikin kasa.
Masana a fannin tsaro na yanar gizo da harkar kudi sun bayyana cewa akwai bukatar gwamnati ta karfafa matakan da take dauka wajen hana yaudarar jama’a, kasancewar har yanzu mutane da dama na ci gaba da fadawa tarkon kamfanonin da ke amfani da dabarun jawo hankali da alkawurran karya.