
Gwamna Zulum a garin Marte da Boko Haram ke yiwa barazana
Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana dalilin ya sa ya kwana a garin Marte duk da fargabar ‘yan Boko Haram.
Zulum ya ce, ya kwana ne domin ƙarfafa wa jama’ar garin gwiwar ci gaba da zama a cikinsa, sakamakon kazamin harin da mayakan Boko Haram suka kai a makon jiya
“Aƙalla mutane 20,000 ne suka gudu daga garin domin tsira da rayukansu… mu kuma ba zamu taɓa barin garin ya faɗa hannun ƴanta’addan ba.” in jin gwamnan.
Gwamnan ya kuma ce, aƙalla garuruwa 300 da ke yankin suka tashi saboda hare-haren ƴan ta’addan, saboda haka gwamnatinsa ke ɗaukar matakan da suka dace tare da jami’an tsaro domin kare lafiya da dukiyoyin mutanen Marte.
Gwamnan ya kuma buƙaci taimakon gwamnatin tarayya domin tinkarar wannan matsala, musamman la’akari da yadda hare-haren mayaƙan suka karu a wannan lokaci.
Jihar Borno na ci gaba da fuskantar ƙarin hare-hare Boko Haram, musamman a ƴan kwanakin da suka gabata.
A makon jiya kawai, mayaƙan sun kai hare-hare aƙalla sau 6 a garuruwa daban daban, wanda ya ritsa da jami’an soji da kuma fararen hula.