
Kwamishinan ’Yan sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ya bayyana dalilin jami’an tsaro na hana hawan sallah da aka saba na al’ada.
Kwamishinan ya fadi hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a wani taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar rundunar da ke Bompai a ranar Juma’a.
“Haka kuma an haramta duka wasu nau’ikan hawan sallah da duk wata kilisa ta dawakai ko tseren mota a lokacin bukukuwan sallah ƙaramar da ke tafe,
“Mun ɗauki wannan matakin ne sakamakon rahotonnin tsaro da muka samu da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, domin tabbatar da zaman lafiyar al’ummar jihar.” In ji Kwamishinan.
Sanarwar Kwamishinan ta ce, rundunar ta baza jami’anta a sassan jihar domin tabbatar da bin doka da oda a jihar, kafin sallah da lokacin bukukuwan bayan sallar.
Kwamishina ya shawaraci mazauna jihar da su gudanar da sallar idinsu cikin kwanciyar hankali da lumana, yadda aka saba, ba tare da tashin hankali ba.
“Don haka muna kira ga al’umma da su kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa”, in ji sanawar.
Aminiya ta rawaito cewa, hakan na zuwa ne bayan da jama’a suka zura ido suna jiran ganin Sarki Muhammadu Sanusi II zai yi hawan sallah a jihar, bayan Sarki Aminu Ado Bayero ya sanar da janye hawan saboda dalilai na tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Ko a shekarar da ta wuce, ’yan sanda sun haramta hawan Sallah sakamakon taƙaddamar masarautar jihar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.