Daya daga cikin wadanda suka assasa masana’antar Kannywood Malam Tahir Fagge ya bayyana dalilan da suka sa Masana’antar ta sauka daga kan layi, wanda hakan ke ci gaba da kawo ci baya ga harkar fina-finan Hausa.
Kannywood ta kasance babbar masana’antar dake samar da fina-finan harshen Hausa a Duniya, inda ta shahara da manyan ‘yan wasa da mawaka wadanda duniya ta dasu.
A wata hira da manema labarai, tsohon jarumin Tahir Fagge ya ce tun farko an gina Kannywood kan wasu manyan tubala da suka hada da kaunar juna, bayar da shawarwari, shugabanci nagari, amma yanzu an rasa wasu daga ciki saboda zuwan zamani da sauran dalilai.
Ya kara da cewa a baya duk wani dan Kannywood na matukar son ganin dan uwansa ya samu ci gaba, idan kuma wata matsala ta faru gare shi, za a jajanta masa, sannan idan akwai wani taimako da wasu zasu iya yi wajen fitar da wannan damuwa to zasu yi, ba kamar yanzu da kowa-kan-sa ya sani ba.