
Shugaban na NNPP ya kuma kira ‘yan majalisa da zama ‘yan amashin da shatan Shugaba Tinubu.
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana matakin da Shugaban Tinubu ya dauka na dakatar da Gwamnan Jihar Ribas da rushe zababbun ‘yan majalisar dokokin jihar ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, a ranar Juma’a.
“Na bi diddigin rikicin siyasar da ke faruwa a Jihar Ribas cikin kwanaki biyu da suka gabata… dalilin shiruna tun farko shi ne kokarin ganin hukumomi da bangarorin da abin ya shafa sun dauki matakin da ya dace”.
“Sai dai abin takaici ne yadda Shugaba Tinubu ya dauki wannan mataki na dakatar da Gwamna Fubara da mataimakiyarsa, tare da rushe majalisar dokokin jihar ba tare da bin tanadin kundin tsarin mulki ba”. in ji shi.

Kwankwaso ya ce, abin da ya fi damunsa shi ne yadda majalisar kasa na wakilai da dattawa suka gaggauta amincewa da wannan mataki ba tare da cikakken nazari ba.
“Matakin ya raunana dimokuradiyya, kuma bisa dukkan alamu, an yi gurguwar fahimta kan sashi na 305(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999”. In ji Sanata Kwankwaso.
Tsohon Sanatan yayi gargadin cewa, idan ba a dakatar da wannan mataki ba, zai iya haddasa rashin bin doka da kuma al’adar yin hukunci bisa son rai a kasar.