
Magoya bayan jam’iyyun adawa a Ghana za su tsunduma zanga-zangar ƙasa baki ɗaya domin nuna adawa da dakatar da Aƙalin alƙalan Ƙasa, Gertrude Torkornoo.
Jam’iyyun da za su gudanar da zanga-zangar sun haɗa da NPP da Liberal Party of Ghana da NDP da PNP da kuma Ghana Union Movement.
Shugaban ƙasar, John Mahama ne ya dakatar da Torkornoo a ranar 22 ga Afrilu, bayan karɓar ƙorafe-ƙorafe guda uku da ke neman a tsige ta, duk da cewa ba a bayyana tuhumar da ake yi mataba.
An nada Torkornoo ne dai a watan Afrilu na shekarar 2023, inda ta zama mace ta uku da ta riƙe wannan muƙami tun bayan samun ‘yancin kai da Ghana ta yi a shekarar 1957.