An kubutar da ‘yan makaranta mata dalibai 25 da ‘yanbindiga suka sace a makarantar sakandare ta Maga jihar Kebbi.
An sako daliban ne a ranar Talata da maraice.
Rahotanni sun ta tabbatar da sakin ɗaliban bayan sasanci da Gwamnatin Tarayya ta yi ta hannun Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu da Hukumar Tsaron ta Farin Kaya (DSS), waɗanda suka jagoranci tattaunawa da ɓangarorin da abin ya shafa.
- Za Mu Dauki Dukkan Matakai Don Ceto Daliban Kebbi – Gwamnatin Tarayya
- ‘Yan ta’adda sun sace dalibai 25 sun hallaka shugaban makaranta a Kebbi
Rahotanni sun ce gwamnati ta yi amfani da tsarin lumana ta hanyar sulhu ba tare da amfani da ƙarfin soja ba, wanda ya haɗa da tattaunawa wajen kuɓutar da ɗaliban.
‘Yan bindiga sun sace daliban 25 ne da asubahin ranar Litinin ta makon jiya ce a harin da suka kai Makarantar Sakandiren ’Yan Matan ta GGCSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu a Jihar Kebbi, inda suka yi awon da ɗaliban ke shirin tashi sallar asuba.
