Indiyawa masu aikin ummara 42 sun mutu sakamakon hatsarin mota da ya faru kan hanyar Madina zuwa Makka
Rahotanni sun ce lamarrin ya faru ne ranar Litinin da misalin 1:30 na dare agogon Saudiyya.
A lokacin da wata motar safar suke ciki mai dauke da fasinjoji 43 ta yi taho-mu-gama da wata tankar mai.
Rahotanni sun ce mutum daya ne ya tsira da ransa daga cikin fasinjojin, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Indiya Dakta S.
Jaishankar ya wallafa a shafinsa na X.
“Ofisoshin jakadancin kasar a Riyadh da Jeddah suna bayar da cikakken tallafi ga Indiyawan da hatsarin ya rusta da su.” In ji shi.
Jakadan ya kuma aike da sakon ta’aziyya ga iyalai da ‘yan’uwan wadanda suka mutu a hadarin.
