Daga Ahmad Adamu Rimingado
Kungiyar tsoffin daliban Jami’ar Bayero Kano (BUK Alumni) ta gudanar da taron sada zumunta karo na 35 a ranar Asabar, 6 ga Satumba, 2025 a Convocation Arena, sabuwar jami’ar.
Taron ya samu halartar tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Ministan Ilimi, Malam Ibrahim Shekarau, wanda ya jaddada muhimmancin tsoffin dalibai wajen bayar da gudunmowa ga makarantun da suka yi karatu domin inganta harkokin koyo da koyarwa.
Shekarau ya ce akwai bukatar tsoffin dalibai su rika waiwayen makarantunsu, su dauki nauyin gyare-gyare tare da samar da kayayyakin da ake bukata, domin taimakawa dalibai masu tasowa su samu ilimi mai inganci. Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su kara tallafa wa fannin ilimi domin rage radadin matsalolin da gwamnati ke fuskanta daga matakin firamare har zuwa jami’a.
Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Haruna Musa, ya bayyana cewa jami’ar a shirye take ta hada hannu da kungiyar tsoffin dalibai wajen aiwatar da manufofin da za su ciyar da makarantar gaba.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar tsoffin daliban, Shu’aibu Abubakar Idris, ya ce sun riga sun kashe miliyoyin naira wajen samar da ruwa domin amfani da dalibai. Ya kuma kara da cewa kungiyar na da shirin tara kimanin Naira biliyan 500 a nan gaba domin gudanar da manyan ayyuka a jami’ar.
Sakataren kungiyar, Malam Salisu Indabawa, ya ce sun shirya tsaf domin tallafawa jami’ar a kowanne fanni.
Bayan kammala taron, Farfesa Haruna Musa ya kaddamar da sabon shafin yanar gizo na kungiyar tsoffin daliban jami’ar wanda kowanne tsohon dalibi zai iya shigar da bayanansa domin zama mamba: 👉 www.bukalumni.org.ng.
Taron ya kuma samu halartar uban jami’ar, AVM Saddik Isma’il Kaita, wanda ya tabbatar da cewa jami’ar za ta ci gaba da inganta fannin koyo da koyarwa, tare da samar da sababbin darussa da bunkasa bincike.
Tsoffin dalibai daga fadin kasar nan da manyan baki ne suka halarci wannan gagarumin taro.
