Dan Majalisa mai wakiltar Bebeji da Kiru a Majalisar Wakilai ya ce ba a fahinci matsayinsa bane kan kudurin dokar haraji da ake ta cece-kuce a kanta.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata kan matsayinsa a muhawarar da ake yi kan dokar da aka ce ya bayar da amanna duk da sukan da ta ke sha.
“Ban ce na goyi bayan ƙudirin gyaran dokar haraji ɗari bisa ɗari ba, ina bada hakuri na rashin fahimta da aka yi. Abin da nace, akwai batutuwa da dama waɗanda za su zama alheri ga Arewa da Nigeria, ba komai ne za a yar ba, akwai abubuwan da za a amfana…” Inji shi.
Ya kuma ce, ‘yan Majalisa na yankin su yi amfani da rinjayen su, su tsaya su goyi bayan duk wasu ƙudirorin da za su amfani yankin ta fannonin bunƙasa tattalin arzikin yankin, waɗanda ke cikin ƙudirorin. Su kuma cire waɗanda za su cutar ko su gyara ta yadda ba za ta cutar da arewan ba.
Ya kuma ce, a matsayinsa na wanda ya dade a majalisa bai taɓa goyon bayan duk wata doka ko ƙudirin da zai kawo illa ga mazaɓa sa ta, da jihar Kano ba, ballantana arewa ko Nigeria.
Daga karshe dan majalisan ya jama’a hakuri na irin fushin da ya aka yi da shi kan matsayin nasa wanda ya kira na rashin fahimta ne.
A baya dai an rawaito dan majalisar na furta wasu kalamai da suke nuna goyon bayan kudurin dokar mai sarkakiya da masana suka ce akwai tanade-tanaden da za su cutar da arewa.
Wanda hakan ya janyo kiraye-kiraye na a janye dokar tare yin Allah wadai ga wadanda suke goyon bayanta