Kungiyar agaji ta Save the Children ce ta bayyana barnar da cutar kwalarar ta yi inda mutane 70 a suka mutu a cikin mako guda.
Cutar ta fi kamari a jihar White Nile dake kudancin Khartoum, inda ake ci gaba da yaki a kasar wanda ya daidaita rayuwar dubban mutane.
Bincike ya nuna cewa, barkewar cutar na da nasaba da wani hari da jirgi maras matuki ya kai kan tashar samar da wutar lantarki, wanda hakan ya haddasa karancin tsaftataccen ruwan sha a yankin.
A cewar kungiyar agajin, yara ne suka fi shan wahala a wannan rikici da aka shafe sama da shekaru biyu ana gwabzawa, inda keɓantattun cututtuka da matsananciyar yunwa ke kara barazana ga rayuwarsu.
Jihar White Nile na daga cikin yankunan da ake samun hauhawar tashin hankali a kwanakin nan, lamarin da ke kara ta’azzara halin da jama’a ke ciki.
