Muhawara ta barke a fagen siyasar kasar nan bayan wata ganawa da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya yi da tsohon shugaban kasa Good Luck Ebele Jonathan.
Jiga-jigan ‘yan siyasan sun gana ne a ne a birnin tarayyar Abuja, inda Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasar Good Luck Jonathan har gida.
‘Yan siyasar biyu basu bayana abubuwan da suka tattauna ba, amma mutane da dama na alakanta ganawar ta su da shirye-shiryen tunkarar zaben shugaban kasa na 2027 mai zuwa.
Ana rade-radin cewa dukkansu, na sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2027 mai zuwa.
Atiku Abubakar na cikin wadanda suka jagoranci kifar da gwamnatin Good Luck Jonathan a zaben 2015 a a karkashin jam’iyyar APC
