
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da cewa sama da mutum miliyan daya ne suka kammala rajistar katin zabe ta internet a cikin mako daya da bude shafin rajista.
Wannan adadi ya fito ne daga ranar 18 zuwa 24 ga watan Agusta, kamar yadda Kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin wayar da kan jama’a, Sam Olumekun, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
A cewar INEC, jihar Osun ta fi kowacce yawan masu rajista da mutum 393,269 sai Lagos da ke biye da 222,205 yayin da Kano ke da 10,166 da Jigawa ke da 8,243.
Jihar Ebonyi ce ta fi kankanta da 261 kacal.
Rahoton ya kuma nuna cewa mata sun fi maza yawan masu rajista da kashi 52, yayin da maza ke da kashi 48.
Matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34 ne suka fi yawa da kashi 62, inda dalibai suka fi yawan masu rajista a fannin sana’a.