
Kasar China ta gayyaci Kim Jong-un na Koriya ta Arewa da Vladimir Putin na Rasha zuwa bikin faretin soji a Beijing don murnar cikar shekara 80 da kammala Yaƙin Duniya na Biyu.
Shugabannin biyu za su kasance cikin shugabanni 26 da ake sa ran halartar bikin.
Ana sa ran a tattauna yaƙin Ukraine yayin ziyarar, inda ake fatan China za ta taka rawa wajen shawo kan shugabannin biyu kan kawo ƙarshen rikicin.
Ziyarar Putin zuwa China ta kasance ta farko cikin shekaru shida.