
Gobarar ta tashi ne cikin dare bayan gama girki da murhun da ba a kashe wutar ba.
Wutar ta tashi ne a garin Satigal da ke Karamar Hukumar Bunkure a Jihar Kano a Laraba dadaddare.
A hirarsa da wakilinmu Rabi’u Kura Jami’in Yaɗa Labarai na shiyyar Rano ya ce, duk da mazauna yankin sun haɗa kai wajen kashe gobarar da kuma ceton rayuka, gobarar sai ta yi barna ga gidaje da kuma dukiya
Hakimin Satigal, ya jagoranci wasu mazauna yankin zuwa wajen sarkin Rano inda suka bayyana cewa gobarar ta lalata gidaje guda shida, kaya, hatsi, dabbobi da kuma wasu kayayyakin amfanin yau da kullum da darajarsu ta kai ta miliyoyin Naira.
Sarkin ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa kuma ya ba su tallafin Naira 200,000 domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi.