
Tsarin biyan harajin zai soma aiki ne a farkon watan Maris ga duk kudin da aka cira a ATM na ciki da wajen banki
Babban Bankin Najeriya CBN ya sa haraji kan kudin da aka fitar ta hanyar katin kati ATM
Sanarwar hakan na kunshe ne a wata sanarwa daga Bankin mai dauke da hannun shugabanta da ta karade shafukan sada zumunta a yammancin Talata.
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya shirya fara sabon tsarin cajin kudade kan ma’amalolin ATM daga ranar 1 ga Maris, 2025.
Ga yadda sabon tsarin zai kasance:
– ATM da ke cikin banki (On-site ATMs): Za a caje Naira 100 kan duk cire kudi har N20,000.
– ATM da ke wajen banki (Off-site ATMs): Za a caje Naira 100 tare da karin caji da ba zai wuce Naira 500 ba kan duk cire kudi har N20,000.
– ATM na bankin da aka buɗe asusu a ciki (On-Us transactions): Ba za a caje komai ba idan kwastoma ya cire kudi a ATM na bankinsa.
Wannan sabon tsari yana da nufin samar da daidaito a tsarin hada-hadar kudi a Najeriya, in ji sanarwar