CBN ya gargaɗi Bankuna kan boye kudi
Bankin na CBN ya yi gargaɗin cewa zai hukunta duk bankin kasuwancin da aka samu da laifin ɓoye Naira ko kuma karkatar da su zuwa wani wurin.
Gargadin na zuwa ne duk bayan da korafe-korafe ya yi yawa kan rashin takaradun kudin duk da yawan tsabar kudin da ke zagayawa tsakanin al’umma.
Bankin ya ce, tsabar kudin da ke hannun jama’a yawansa ya kai Naira tiriliyan 4 da biliyan 200 da 9 wanda ke matsayin kashi 94.3 na jumullar tsabar kudin da ake hada-hada da su a kasar.
Bayanai sun ce CBN ya kara yawan takardun kudin da ya ke fitarwa duk shekara zuwa Naira Tiriliyan guda da rabi, sai wannan bai hana wasu yankuna fuskantar ƙamfar takardun kuɗin ba.
Wanda ya ce ba zai lamunci hakan ba.
