Rundunar sojin saman ta ƙasa ta tura wata tawaga mai karfi zuwa jihar Zamfara domin yin bincike kan zargin yin barin wuta bisa kuskure akan fararen hula.
A ranar Asabar aka ruwaito cewa Sojin Sama sun yi ruwan wuta kan al’ummar gari a ƙauyukan Kakindawa dake Ƙaramar Hukumar Maradun, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar ‘yan sa kai 16.
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin saman ta fitar a yammacin Litinin ta ce, Air Vice Marshal Edward K Gabkwaet ne ya jagoranci tawagar binciken.
Mai Magana da yawun rundunar sojin AVM Olusola Akinboyewa ya ce, ‘yan kwamitin binciken zai gana da masu ruwa da tsaki domin tattauna lamarin tare da gano sahihin abin da ya faru.