Jakadan China a Najeriya Yu Dunhai ya kai ziyara ga Mai Bai wa Shugaban kasa Shawara Kan Tsaro Malam Nuhu Ribadu a ofishinsa da ke Abuja.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis,
“A shirye China take ta taimaka wa Najeriya wajen murkushe ta’addanci da daidaita al’amura a kasar.
“China tana adawa da duk wani katsalandan cikin al’amuran wata kasa na cikin gida da sunan addini da ‘yancin dan’adam”. In ji shi.
Jakadan ya kuma kara da cewa, chaina na adawa da barazanar takunkumi da amfani da karfi.
Ziyarar jakadan ta China a Najeriya na zuwa nebayan Ma’aikatar Harkokin Wajen China ta bayyana adawa da Trump kan amfani da addini da hakkin dan’adam wajen tsoma baki a harkokin kasar.
