
Jami’ar Bayero ce ta zo ta daya a daukacin jami’oin arewacin kuma ta uku a jerin jami’oin Najeria.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin sabon rahoton Times Higher Education na World University Rankings na shekarar 2026
A cewar rahoton binciken da aka wallafa ranar Alhamis, Jami’ar Bayero ce tana cikin rukuni na 1001–1200 a duniya, yayin da ABU Zaria ke cikin 1201–1500, abin da ke nuna karuwar tasiri da ci gaba a fannin bincike da koyarwa a jami’o’in Arewa.
BUK ta samu matsayi na farko a Najeriya a fannin a ma’aunin dake auna hadin gwiwar jami’a da kasashen waje da yawan daliban kasashen waje da kuma hadin gwiwar bincike da sauran jami’o’i a duniya.
Rahoton na 2026 ya nuna cewa, jami’o’in Arewa na cike gibin tazarar da ke tsakaninsu da na Kudancin kasar nan.
Daga cikin jami’o’i 51 da binciken ya ambato daga Najeriya, akalla 10 daga Arewa ne, ciki har da BUK, ABU, Jami’ar Fasaha ta Minna da Jami’ar Maiduguri da kuma Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tafawa Balewa dake Bauchi.
Jami’ar Ibadan ce ta farko a Najeriya sai kuma Jami’ar Legas (UNILAG), sannan BUK ta zo ta uku. a cewar rahoton