Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ba shi da fili Abuja wanda gwamnati za ta soke izinin mallakarsa.
Kakakin tsohon Shugaban kasa Garba Shehu ne ya karyata yamadidin da ake yi na malakar filin da Ministan birnin ya soke izinin mallakarsa a ranar Alhamis.
.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a matsayin martani ga sanarwar da Ministan Abuja Nyesom Wike ya fitar na jerin a sunanyen mutanen ya soke izinin mallakar filayensu a birnin, a bisa rashin biyan kudin ka’ida.
Ciki har da Muhammadu Buhari, wanda hakan ya janyo cece-kuce kan dacewa da kuma rashin dacewar yin hakan.
Kakakin tsohon shugaban ya ce, filin da ake magana a kai na Gidauniyar Muhammadu Buhari ne wacce wasu masoya shugaban suka kafa da sunansa kuma suka nemi mallakar filin amma ba na kashin kansa bane.
“A matsayinsa na dan kasa yana kan mulkin an rarraba musu takardar mallakar filin na Abuja. amma shi ya dawo na na sa, ya kuma ce a je ba wa wadanda ba su da shi, domin shi tuni ya mallaka”. inji shi.
Sai dai ya ce, Gidauniyar ta nemi mallakar fili amma aka dakile yunkurin nata a Ma’aikatar kula da filaye na Hukumar Raya Babban Birnin FCDA, in da aka caje ta kudi na fitar hankali da ya zarce na sauran kungiyoyi masu zaman kansu.
Wanda hakan ya sa ta hakura. inji shi
Garba Shehu ya yi kira ga masu tayar da jijiyar wuya a dandalin sada zumunta da sauran kafofin yada labarai kan dacewa ko rashinsa na soke izinin filin da aka ce na Buhari ne, su daina.