Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa wasu majiyoyi daga hukumomin tsaro a Abuja sun sanar da shi cewa kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta sanya sunansa cikin jerin mutanen da take shirin kashewa
Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga mabiyansa, inda ya ce ya samu kiran waya daga wani mutum da ya ki bayyana sunansa, wanda ya fada masa cewa an ambaci sunansa a wani taron tsaro na kasa.
A cewarsa, wanda ya kira shi ya sanar da shi cewa sunansa na daga cikin mutanen da aka ambata a matsayin wadanda ake shirin hallakawa.
Sheikh Gumi ya zargi Amurka da hannu wajen samuwar kungiyar Boko Haram.
Malamin ya kuma yi zargin cewa tabarbarewar tsaro da rarrabuwar kawuna da ake fuskanta a Najeriya sun kara tsananta ne sakamakon karya, barna da manufofin da ya danganta da shugaban Amurka, Donald Trump.
