’Yan bindiga sun kashe makiyaya uku tare da hallaka shanu kusan 50 a yankin Aloghom da ke ƙaramar hukumar Mangu a jihar Plateau.
Harin ya faru ne kwana guda bayan rahoton kashe wani makiyayi mai suna Yakubu Ishaku a yankin Nyerwe, da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta jihar.
Mai kula da ƙungiyar Fulbe Fulani Development Association a Mangu, Hashimu Yahaya, ya bayyana harin a matsayin mummunan lamari, yana mai cewa an kashe mutanen ne yayin da suke gudanar da harkokinsu na kiwo.
Shi ma shugaban ƙungiyar Miyetti Allah ta MACBAN, na jihar Plateau, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ’yan bindigar sun shiga wurin kiwon ne tare da buɗewa makiyayan wuta yayin da suke kula da shanunsu.
Babayo ya yi Allah-wadai da harin, tare da kira ga makiyayan jihar da su kwantar da hankalinsu, su kuma ci gaba da bin doka da oda.
Kawo yanzu dai Kakakin rundunar Operation Safe Haven, Kyaftin Polycarp Oteh, bai ce uffan ba ga Wakilinmu, bayan ya nemi ƙarin bayani kan lamarin.
