Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa Ta Kasa (NEMA) ta aike da kayayyakin agaji domin bayar da agajin gaggawa ga wadanda iftila’in jihar Benuwe ya shafa.
Babbar Daraktar hukumar ta kasa Zubaida Umar ce aike da kayan tallafin ya biyo bayan bayanan da suka iya dauka na wadanda lamarin ya shafa, da kuma la’akari da halin bukatar tallafin da suke ciki a yanzu.
Zubaida ta kara da cewa sun tattara bayanan wadanda abun ya shafa ne ta hanyar hadin qwiwa da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Benue, sai kuma kungiyar Agaji ta Red Cross da sauran wasu hukumomin bayar da agaji.
Shugabar ta kuma kaddamar da ofishin hukumar na shiyyar Arewa ta tsakiya, a karkashin jagorancin Daraktan shiyyar Mista Aliyu Waziri, don sanya ido kan yadda za a raba kayan tallafin tare da hadin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Benuwe.
Shugabar hukumar, a cikin wata sanarwa da shugaban sashin yada labarai, Manzo Ezekiel, ya fitar a daren ranar Talata, ya kuma ba da umarnin a tantance yawan mutanen da abin ya shafa da kayayyakin more rayuwa da suka salwanta domin sanin karin tallafi da ake bukata.
Kayayyakin agajin da aka baiwa al’ummar sun hadar da buhunan shinkafa da masara, taliya da man girki da sauransu.
Kawo yanzu sama da mutane dubu 3 ne suka yi kaura daga muhallansu biyo bayan hare haren, cikinsu kuwa har da mata da kananan yara, wadanda yanzu haka ke cikin tsananin bukatar abinci magani da sauran kayayyakin bukatun yau da kullum.
