Wani binciken da Premier radio ta gudanar ya gano cewa marasa lafiya da majinyata na fama da matsalar makewayi a asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake Kano.
A ziyarar da wakilan Premier Radio su ka kai asibitin, sun gano bandakunan ba sa shiguwa, yayin da wasu ke kewayawa bayan motoci su na biyan bukatunsu.
Asibitin na Murtala, shi ne babban asibiti a Kano wanda yafi karbar marasa lafiya masu tarin yawa a kowace rana.
Sai dai marasa lafiya da majinyata na ganin ta kansu sakamakon rashin tsaftar wasu daga cikin bandakunan asibitin, sannan ga wari da yake addabar wuraren da bandakunan suke.
A lokacin da Wakilan Premier Radio suka isa daya daga cikin dakunan kwanciya na maza da yake bangaren babban daki na asibitin sun ji wani wari ya turnuke dakin tun daga farfajiyar wurin, sakamakon ruwa baya tafiya, sannan kuma wasu ramuka na masai sun bude.
Wasu majinyata da muka tattauna da su sun koka game da rashin tsaftar bandakunan asibitin, wanda hakan na iya sanya majinyata su kamu da wasu cututtuka na daban.
Asibitin na Murtala na karbar marasa lafiya daga jihohin kasar nan daban daban kai har ma daga makwaftan kasashe.
Majinyatan sun shaida mana cewa a lokuta da dama basa iya biyan bukatarsu a cikin asibitin, har sai sun fita waje.
Wata majinyaciya da ta bukaci a sakaye sunanta ta shaida amana cewa a duk lokacin da za ta shiga bandakin sai ta yi amfani da mayani don toshe hancinta saboda doyi, yayin da a wani lokacin bata iya shiga bandakin.
Haka ma abun yake a bangaren mata, domin kuwa abun ba’a cewa komai,lamarin babu kyan gani ko kadan,tun daga bakin kofar bandakin muka fara yin arba da wani ruwa mai dankareran zarni daya mamaye harabar bandakin.
Haka ma abun ya ke a cikin bandakunan domin kuwa shigar mu ke da wuya muka yi tozali da bayan gida,wanda ya yiwa
bandakin kwalliya, abun dai sai wanda ya gani.
Ko muka tambayi wasu mata masu jinya da basu bada izinin a dauki muryar su ba shin ko ya suke amfani da bandakunan a irin wannan yanayin, cewa suka yi a haka suke shiga, wanda kuma ba zai iya ba ya tsuguna a bayan mota ya biya bukatarsa.
Asibiti dai waje ne da marasa lafiya ke zuwa domin samun lafiya, sai dai kuma lalacewar matsugunan asibitin na zama babbar barazana ga wadanda ke shiga asibitin.
Babban abun tambaya a nan shi ne, shin ko mahukuntan asibitin sun san halin da bandakunan ke ciki?
Shin ko ina ma’aikatan da suke da alhakin kula da wadannan bandakuna?
Sai zuwa yaushe za a gyara wannan matsala?
Zaku ji amsar wadannan tambayoyi a rahotanmu na gaba.