
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar wa jama’a cewa ta tanadi cikakkun matakan tsaro domin gudanar da bikin Takutaha cikin kwanciyar hankali, wanda zai fara daga gobe 12 ga Satumba.
A cikin sanarwar da Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya taya al’ummar Kano murnar bukukuwan, tare da tabbatar da cewa jami’an tsaro zasu yi aiki domin tabbatar da zaman lafiya yayin bikin.
Rundunar ta gargadi masu neman tada rikici domin yin barna, ciki har da fadan daba da fashi da makami.
Rundunar ta ce duk wanda aka kama yana kokarin tayar da zaune tsaye za a gurfanar da shi a kotu.
Kwamishinan ya yi kira ga jama’a da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i domin dorewar zaman lafiya da ci gaban Kano da Najeriya gaba ɗaya.