Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, bayar da tallafin kudin mota gav mutane 710, wanda ba ’yan asalin jihar domin tafiya garuruwansu don gudanar bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.
An ƙaddamar da wannan shiri ne a tashar mota ta Borno Express jiya Asabar, inda aka fara jigilar mutane 285 zuwa wurare daban-daban a faɗin kasar nan.
Za a ci gaba da wannan jigilar, inda za a sake tashin wasu 285 a yau Lahadi, yayin da sauran za su bar Maiduguri gobe Litinin.
Da yake magana yayin ƙaddamar da shirin, shugaban ƙungiyar Ohaneze na jam’iyyar APC, Cif Ugochukwu Egwidike, ya ce kowanne daga cikin matafiya 710 zai shiga mota kyauta tare da kuɗi Naira dubu hamsin.
Haka kuma, mata kimanin dari biyu da hamsin da mazansu suka mutu, kuma ba za su iya tafiya ba, an tanadar musu Naira dubu hamsin domin kowacce ta yi bikin kirsimeti.
Cif Egwidike, ya yabawa Gwamna Zulum wajen tallafawa mabuƙata, inda ya ce shirin zai rage raɗaɗin talauci tare da walwalar al’umma.