Aƙalla mutane 19 ne suka rasa rayukansu, yayin da fiye da 66 suka jikkata a wani mummunan farmaki da Rasha ta kai kan wani dogon gini a yammacin ƙasar Ukraine, ta amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.
Jami’an Ukraine sun ce hare-haren, waɗanda suka faru cikin daren jiya Laraba, sun kuma ritsa da tashoshin samar da lantarki da wasu muhimman sassa da ke da alaƙa da sufuri.
An bayyana cewa Rasha ta harba jirage marasa matuƙa fiye da 470 da makamai masu linzami 48 a cikin wannan sabon luguden wuta.
Hare-haren sun tilasta wa Poland rufe wasu manyan filayen jiragen saman ta biyu da ke kudu maso gabashin ƙasar, saboda tasirin tsaro da farmakin ya haifar.
Sabon luguden ya zo ne a daidai lokacin da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya tafi Turkiyya domin tattaunawa da Shugaban ƙasar, Recep Tayyip Erdogan, a ƙoƙarin farfaɗo da tattaunawar sulhu da aka daina yi tsakaninsu da Rasha.
Zelenskyy ya bukaci abokan hulɗar Ukraine su matsa wa Rasha lamba domin kawo ƙarshen yaƙin da ya shafe kusan shekaru huɗu tana yi a ƙasar.
