
Wani tsohon gida da ya rushe a Legas
Wani gida bene mai hawa uku ya rushe a unguwar Sabon garin Kano, ya kuma hallaka mutane hudu da jikkata Bakwai.
Shugaban Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta ƙasa NEMA, mai da jihohin Kano da Jigawa, Dakta Nuraddeen Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN yau Litinin a Kano.
“Hukumar ta samu kiran gaggawa a yammacin ranar Lahadi 13 ga Yuli, da misalin ƙarfe 6:49, cewa wani bene mai hawa uku da ba a kammala ba ya rushe a unguwar.” In ji shi.
Abdullahi ya ce, lamarin ya faru ne bayan mamakon ruwan sama da aka shafe tsawon lokaci ana yi a karshen makon nan.
Ginin na kan titin Abedi ne a unguwar Sabon Gari ka da ke jihar Kano.