Wani bene mai hawa uku ya rufta inda coma yayi ajalin aƙalla mutum biyar a jihara Legaa.
Lamarin ya faru ne Haɗarin ya faru ne a unguwar Ojodu-Berger da ke Jihar Legas da kimanin misalin ƙarfe 09.45 na safiyar ranar Asabar.
Hukumar Kai Dauki Gaggawa (LASEMA) tare da taimakon ’yan sanda suka gano cewa wani gini mai hawa uku na ɗauke da gidan abinci da kuma mashaya a saman benen.
Jami’in hukumar bayar da agajin na jihar Ibrahim Farinloye ya ce, daga faruwar lamarin yanzu an ceto mutane 20 jimilla da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzan ginin.
Babban Sakataren hukumar LASEMA Olufemo Oke-Osanyintolu ya ce, mamatan biyar da aka samu an killace su a ɗakin ajiyar gawawwaki na asibiti.
“Da farko ana zaton babu wadanda suka mutu sai dai an samu asarar dukiya, amma bayan ci gaba da aikin ceto, an gano gawawwaki a cikin waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin baraguzai.” In ji shi.
’Yan sanda da hukumar kai dauƙin gaggawa sun ci gaba da bincike domin gano musabbabin rugujewar ginin.
Jami’ai na hukumar LASEMA na ci gaba da binciken baraguzan ginin da nufin gano ko da sauran mutane a ciki.
