Hukumar Kula Da Zirga Zirgar Ababen Hawa Ta Jihar Bauchi (BAROTA) ta ce, ba za ta lamunci yadda wasu daga cikin al’umma suke afkwa jami’an hukumar ba, da kuma zargin gaza gudunar da aiki bisa rashin kwarewa.
Mukaddashin shugaban hukumar, Aminu Musa Aliyu ne ya bayyan hakan a hirarsa da manema labarai domin bayyana irin yadda hukumar take ci gaba da gudunar da ayyukanta a jihar.
“Baya ga tsaftace jihar, gwamnati ta samar da hukumar ne, domin samarwa da matasan jihar ta Bauchi aikin yi a hukumar ta BAROTA.
Mukaddashin shugaban ya kuma ce, a yanzu haka suna ci gaba da aiki tare da daukacin hukumomin tsaro dake jihar domin kamo bata garin da suka afkwa jami’an hukumar akan titin Ajiya Adamu dake cikin garin Bauchi har suka jikkata wasu daga cikin jami’an hukumar.
