
Wani jirgin saman kamfanin Saudia Airlines dauke da mahajjata 442 daga Jeddah zuwa Jakarta, ya yi saukar gaggawa a ƙasar Indonesiya bayan samun sakon barazanar bam a jirgin
Lamatrin ya faru ne a ranar Talata a inda Jirgin mai dauke da alhazan ya yi saukar da safe a filin jirgin sama na lardin North Sumatra, inda aka kwashe dukkan fasinjoji cikin koshin lafiya, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
Kwamishinan ‘Yansanda na lardin, Whisnu Hermawan, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun kammala binciken kwakwaf a cikin jirgin da kuma bincike jakunkunan fasinjoji domin tabbatar da tsaron lafiyar mahajjatan da kuma ma’aikatan jirgin.
Kamfanin jirgin na Saudiyya ya bayyana cewa an fara shirye-shiryen tura fasinjojin zuwa inda suka nufa ta wasu hanyoyin daban.
Rahoton ya zo a daidai lokacin da alhazai ke ci gaba da komawa kasashensu bayan kammala aikin hajji bana, lamarin da ya ƙara jaddada bukatar tsaurara matakan tsaro a filayen jirgin sama da sauran cibiyoyin sufuri