
Wasu daga cikin daliban a yayin bikin daukarsu a Jami'ar Tarayya ta Dutsin Ma
Daliban za su yi karatu ne a Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutsin Ma, a karkashin Gidaunyar Barau I. Jibrin
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Barau Jibrin ya dauki nauyin karatu dalibai 1,000 ‘yan asalin jihar Kano.
An kuma yi bikin daukar daliban tare da sauran wadanda suka samu nasarar shiga Jami’ar a daga wasu wurare a harabarta a garin Dutsin Ma a jihar Katsin a ranar Talata.
Bikin da ya samu halartar manyan baki daga ciki da kuma wajen jihar, ciki har da Shugaban Ma’akatan Sanatan wanda ya wakilci Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijan da kuma sauran manayan magoya bayansa.
A kwanan baya ne Sanata Barau ya dauki nauyin wasu karatun wasu daliban zuwa kasashe waje don yin karatu digiri na biyu duk a karkashin Gidauniyar Barau I. Jibrin
A wani mataki na inganta ilmin ‘yan jihar Kano musamman wadanda suka fito daga yankin Kano ta Kudu .